Mutane sun mutu, yayin da Sojoji da Yan bindiga suka shafe awanni suna gumurzu a Kaduna

Dakarun sojin Najeriya sun yi gumurzu da wasu yan bindiga a UnguwanMusa Tudun Wada Kudansa dake Maraban Rido, karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna.

Daily trust ta rahoto cewa sojojin sun fafata da yan ta’addan ne da sanyin safiyar yau Talata, 18 ga watan Janairu, 2022. Kowane bangare tsakanin sojojin da kuma yan bindigan an musu ɓarna, lamarin da ya jefa al’ummar dake yankin cikin tashin hankali.

Meya haddasa musayar wutan?

Basaraken dake yankin, Joseph Sauri Garba, wanda ƴa tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai, yace gumurzun ya shafe awanni uku ana fafatawa tsakanin sojojin da yan bindiga. Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindigan sun farmaki yankin ne da tsakiyar dare da mummunan nufin su na sace mutanen dake rayuwa a wurin. A baya-bayan nan, gwarwazan dakarun sojin Najeriya sun kwato kusan mutum 10 da yan bindiga suka sace a yankin.

Yan sanda sun samu rahoton abinda ya faru?

Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ta wayar salula, bai ɗaga kiran ba, bare a ji ta bakin hukumar su. Yan bindiga, waɗan da gwamnatin tarayyan Najeriya ta ayyana su a matsayin yan ta’adda, suna cigaba da ƙaddamar da hare-hare a ƙauyukan jihar Kaduna, dake arewa maso yamma.


Posted

in

by

Tags:

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *