Iyayen amarya sun fasa aurawa ango ‘yarsu bayan ganin gidan da za ta zauna

Dangin amaryar da ba su so yadda gidan surukinsu yake ba sun gwammace su taimaka masa da wani gidan daban Ango da danginsa da suka ji an raina musu hankali sun ki amincewa da wannan bukatar, nan take dai aka datse batun bikin ‘Yan Najeriya da dama a kafar Facebook sun yi martani kan wannan lamarin da ya faru ya kuma basu matukar dariya.

Wata budurwa ‘yar Najeriya mai suna Maryam Shetty a Facebook ta yada wani labari a shafinta, inda ta zayyana yadda aka fasa wani aure bayan samun karamar matsala. Kafin ta ba da labarin, budurwar ta rubuta cewa al’adar nuna fifiko ya zama ruwan dare a yankin Arewacin kasar nan kuma iyaye ne ke aiwatar da shi.

Yar mu ba za ta zauna a nan ba

Ta bayyana cewa kafin a soke auren, iyayen amaryar sun ji cewa gidan angon sam bai musu ba, kuma bai dace da matsayin ’yar su ba.

Ango da danginsa sun tubure kan bukatar gidansu amarya Don gyara lamarin zuwa yadda suke so, dangin amarya sun ba su wani sabon gida ga ma’auratan; tayin da ango ya ki amincewa dashi tare da danginsa.

Maryam ta ce mutumin dai ba talaka bane domin shi mutum ne mai tarin ilimi kuma yana da aiki mai tsoka.

Ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, rubutun ya tattara fiye da sharhi 400 tare da dubban dangwale bayan da aka sake yada shi ta shafin Instagram na @instablog9ja.

Leave a Reply

Your email address will not be published.