yaro dan shekara 2 ya koyi yaren jafananci cikin sa’o’i 24

Isaiah Gyamfi yaro ne dan baiwa mai shekara biyu dan kasar Ghana wanda ke koyar da kansa harsuna daban-daban a duniya Yaron mai hazaka zai iya rubutu, kirge cikin Turanci, Sifananci, Faransanci, da warware matsalolin ninkawa da debewa a ilimin lissafi Gyamfi ya koyi yadda ake kirge har zuwa 40 a yaren Jafananci a cikin kasa da sa’o’i 24 bayan kallon bidiyon kidaya na yaren.

Wani yaro dan kasar Ghana mai shekaru biyu, Isaiah Gyamfi, ya koyi yadda ake rubutu da kirge cikin Turanci, Sifaniyanci, Faransanci da warware matsalolin ninkawa da debewa a lissafi. Ya kuma koyi kirge har zuwa 40 a cikin yaren Jafananci cikin kasa da sa’o’i 24, kamar yadda kafar labarai a kasar Ghana, Yen ta ruwaio.

Mahaifiyarsa mai shekaru 30, Jazelle, daga Kudu maso Yammacin London, ta shaida wa jaridar Mirror cewa yaron yakan iya fahimtar sabbin bayanai cikin sauki tun yana dan shekara biyar.

Yadda lamarin ya faro

Mahaifiyar yaron ta tuno yadda danta ke kallon faifan bidiyo a wayarta akan kafar YouTube.

A cewarta:

“Ya gangara zuwa wani faifan bidiyo a can kasa sannan ya lalubo bidiyon lissafin Jafananci.”

Mahaifiyar wacce malamar koyar da yara kanana ne a birnin Landan ta bayyana cewa yaron ya kalli bidiyon ne sau daya, sannan ya gyara zama, kuma ya nemi ya sake saka masa ya kalla.

A kalamanta:

“Sai kuma kafin na ankara, kawai ya fara sake maimaita lambobin daidai.” Lokacin da ta fahimci cewa danta yana sha’awar harsuna, ta ci gaba da nuna masa bidiyo a cikin harshen Sifananci wanda daga baya ta samo masa katunan karatu da yaren. Jazelle ta mayar da falonta ya zama dakin lissafi da karance-karance ta yadda yaron zai amfana sosai idan ya cika wani munzali.

Karatun haruffa

Ya ba iyayensa mamaki yayin da ya karanta harrufa a lokacin da suka nuna masa. Jazelle ta tuna cewa yana iya gane harrufa daidai tun yana dan wata takwas, kuma makonni bayan haka, yakan fitar da amonsu ta hanyar karatun ‘phonics’.

Ta fara tattara bayanan ci gaban da ya samu a kafar Instagram a farkon wannan shekarar. Yanzu ya zama mai girma sanin harsuna. A shafinta na Instagram, ta nuna cewa Gyamfi yana magana da harsuna da yawa: Turanci, Sifaniyanci, Faransanci, Italiyanci, Twi, Yarbanci, da Jafananci. Duk da haka, bai iyakance ga kalmomi ba; yana iya gane tutoci.

Jazelle ta shaida wa manema labarai cewa danta yana son lissafi sosai har yakan koyar da abokansa a makarantar renon yara.

A cewarta:

“Na tuna wani malaminsa na makarantar reno yana gaya mani cewa yakan zauna da abokansa yana taimaka musu su san lissafi.” Iyayen Gyamfi sun shirya kai shi wurin wani masanin ilimin halayyar yara domin a tantance shi saboda sun yi imanin cewa yana da hazaka.

Mahaifiyarsa ta ce. “Ban taba samun gamuwa da yaro kamarsa ba, kuma ina fadin hakan tare da gogewar shekaru 10 a harkar karantar da yara.”

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.