Wani sanannen gurin siyan kayayyaki mai suna Next shopping mall wanda yake a Ahmadu Bello way, Kado ya kama da wuta.
Haryanzu ba’a son musabbabin wutan ba.
Wutan na ta ci yayin da jami’an kwana-kwana ke kokarin kashewa a lokacin da muke kawo muku wannan rahoton.
Wannan ginin an amince cewa na tsohon Gwamnan Anambra ne Peter Obi.
Cikakken bayanai na nan zuwa.