An damƙe wani Alfa ɗauke da kan mutum

Jami’an ‘Yan Sandan Jihar Ondo sun bayyana nasarar kama wani malam-boka mai suna Tunde Olayiwa, wanda aka same shi da kunkurmin kam mutum, wanda ba a jima da guntule shi ba.

An kama Alfa Tunde a cikin ƙaramar hukumar Oka, cikin Jihar Ondo.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Ondo Oyeyemi Oyediran ya shaida wa ‘yan jarida haka a ranar Alhamis, a lokacin da ya ke gabatar da shi da wasu masu aikata wasu laifuka daban-daban, a Akure, babban birnin jihar.

Kwamishinan ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan sanda sun samu nasarar damƙe Alfa ɗin wanda ake zargin cewa su na haɗa asirin yin ƙazaman kuɗi ne, bayan wani ya kwarmata masu abin da Alfa ɗin ke aikatawa a garin Oko.

“Jami’an Yan Sanda sun samu kwarmato daga wani mutum a ranar 23 Ga Disamba, 2021. Mai kwarmato ya shaida cewa wani mai kiran kan sa Alfa Tunde Olayiwola, wanda ake zargin cewa matsayi ne, an ga wani ya kai masa ƙiren dungulmin kan mutum, wanda kuma bai daɗe da gutsirowa ba.

“Nan da nan ‘yan sanda su ka garzaya su ka damƙe bokan a unguwar Ajagbale a Oka, Jihar Ondo.

“An samu ƙiren guntulallen kan mutum a ɗakin sa.

“Da bakin sa ya furta cewa an kawo masa kan ne domin ya yi amfani da shi ya samu ƙarin fatahin rayuwa.”

Kwamishinan ya ce an kama wasu mutum uku bisa zargin kisan kai a tsakanin 17 zuwa 21 Ga Disamba.

Ya ce an kama Ayodele Bankole mai shekaru 26 bayan ya aikata laifi. Ya shiga wani otal da ake kira ‘Enjoy your life” a Adabo Oke-aro, amma sai a ka ga ya diro ta taga ya tsere.

Bayan an kamo shi, an koma da shi cikin otal ɗin, inda aka je ɗakin ana tsinci gawar mace mai kimanin shekaru 24 ta mutu a cikin jini, kuma an ji mata ciwo a wuya da ƙirji.

“An kai ta asibiti, inda aka tabbatar mutuwar matar. Kuma aka samu wata sharɓeɓiyar wuƙa a inda aka kashe ta.

“Shi kuma Paul Samuel an kama shi ne a ranar 20 Ga Disamba, bayan an zarge shi da sace Haruna Sha’aibu domin yin tsafin tara ƙazamar dukiya.

“Da aka kama shi, ya ce shi ya kashe abokin na sa, domin ya mallaki babur ɗin sa.

Leave a Reply