Mata masu juna biyu sun haihu a kan tsaunuka garin gujewa ‘yan bindiga

Kimanin mutane 5,000 na wani yanki a jihar Neja a halin yanzu suna fakewa a wani tsauni saboda barnar ‘yan bindiga. Mutanen da suka hada da yara kanana da kuma tsofaffi suna gujewa kisan gilla ne daga ‘yan bindigar da suka addabi yankin Yayin da suke cikin tsaunuka, wasu mata biyu masu juna biyu daga cikin mutanen sun haihu a cikin mawuyacin hali.

Wasu mata biyu masu juna biyu a jihar Neja sun haihu a kan wani tsauni a lokacin da suke kokarin tserewa hare-haren ‘yan bindiga a yankinsu.

Jaridar Nigerian Tribune ta rawaito cewa harin da aka kai a kauyen Kwimo da ke karamar hukumar Mariga ta jihar Neja ya sa daukacin al’ummar yankin tserewa don tsira da rayukansu.

A cewar wani ganau mai suna Usman Kwimo,

“Ba zan iya tabbatar da halin lafiyar mata masu juna biyun da jariransu ba saboda ba su da kayan aikin jinya da ake bukata don kula da su.”

Kwimo ya ce kimanin mutane 5,000 na al’ummar yankin da suka hada da yara kanana ne ke fakewa a tsaunuka daban-daban a yankinsu da nufin gudun kada ‘yan ta’adda su kashe su. Ya ce ‘yan bindigar da suka kai farmaki kauyen Kwimo akan babura kusan 120 dauke da manyan makamai, suna harbi da bindiga, sun yi awon gaba da kayan shaguna da kayayyakin gida baya ga lalata wasu kadarorin. Da yake mayar da martani ga rahoton, sakataren gwamnatin jihar Neja, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya baiwa al’ummar jihar tabbacin cewa gwamnati a shirye take ta yi duk mai yiwuwa domin kare rayuka da dukiyoyinsu.

Ya ce an shirya jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya a wasu al’ummomin da ke fama da rikici a jihar, kamar yadda gidan radiyon Najeriya da ke Kaduna ya tattaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published.