Kaji masu yi da gaske: wani mutum ya yi wa matarsa kyautar jirgin sama

Masoya biyu ma’aurata, Masoud da Stephanie Shojaee, sun nunawa mutane cewa komai tsufan aure, kada soyayya ta gushe A cikin wani faifan bidiyo da matar ta yada ta yanar gizo, mijin ya ba ta jirgin sama nata na kanta a matsayin kyautar farkon Kirsimeti Wannan kyauta ya jawo cece-kuce a kafofin sada zumunta, inda mutane da yawa suka bayyana ra’ayoyinsu akai.

Shahararrun ma’aurata a kafar Instagram, Masoud da Stephanie Shojaee, sun sa mutane magana yayin da matar ta yada wani gajeren bidiyonta da mijinta. A cikin gajeren faifan bidiyon, an fito da matar ne daga cikin wata mota kirar Rolls Royce yayin da Masoud ya rufe idonta. A gabanta kuwa, ga wani jirgi mai zaman kansa.

Babbar kyauta ga matarsa!

Lokacin da aka bude idonta, sai matar ta rungume mijinta cikin murna da annashuwa. Ta rubuta cewa bayan shekaru 11, mijinta har yanzu ya san hanyar da zai ba ta mamaki da farin ciki.

Stephanie ta bayyana cewa jirgin kyauta ce mai ban mamaki a gare ta. Ta kara da cewa ta so jan kafet da aka shimfida mata a bakin jirgin don karramawa

 

Yaya ba ki suma ba?

Mutane da dama da suka yi sharhi game da wannan kyauta sun yi mamakin yadda ta samu nutsuwa kuma ba ta suma ba da ganin irin wannan babban lamari.

Menene sana’ar wannan miji? Duba ga bayanan mijin ya nuna cewa yana aikin sayar da gidaje ne kuma shine shugaban kamfanin SHOMA GROUP, kamfanin da aka kafa inji bayanansa na Instagram a shekarar 1988. Lokacin da @instablog9ja ya sake yada bidiyon, ‘yan Najeriya sun tofa Albarkacin bakinsu. Wasu dai sun ce mutumin ba wai kawai kai makura yayi a nuna soyayya ba, shi ne ma kololuwa a fannin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.