An kama Magidanci ya kashe matarsa don yaci gadon dukiyar ta

Rundunar ‘yan sanda ta ƙasa ta kama Emeh Kalu wanda ya kashe matarsa Nneka Kalu domin ya ci gadon dukiyarta.

Kakakin rundunar Frank Mba ya sanar da haka wa manema labarai ranar Laraba a Abuja.

Mba ya ce Emeh dan asalin kauyen Nguzu Edda ne dake karamar hukumar Afikpo ta Kudu a jihar Ebonyi.

Ya ce an tsinci gawar Nneka ranar 29 ga Agusta a gonar rogo dake kauyen Nguzu Edda kusa da jihar Abia.

Mba ya ce sakamakon bincike ya nuna cewa Emeh ya lallabi matarta sa zuwa wani wurin inda ya tabbatar babu mutane sannan wasu mutum biyar da ya ba su kwangilan kashe ta suka tafi da ita.

“Kafin su kashe ta sai da suka sa Nneka ta fadi inda takardun kadarorinta suke kaf.

“Rundunar ta fara gudanar da bincike domin gano wanda ya kashe Nneka bayan mutanen kauyen Nguzu Edda sun kawo kara ofishinsu.

“A dalilin binciken da muka gudanar mun samu nasarar kama mutum uku cikin mutum biyar din da suka yi kwangilar kashe Nneka da shi mijinta Ehem.

Ya ce rundunar za ta kai Ehem da mutanen da ya basu kwangilar kashe matarta sa kotu da zarar an kammala yin bincike akai.

Rashin yarda da juna tsakanin ma’aurata na daga cikin matsalolin dake kawo rashin zaman lafiya a tsakanin mace ko namiji a gidajen aure.

Leave a Reply