Akwai yiwuwar a fara wahalar man fetur a gidajen man Jihohin Arewa

Kungiyar ‘yan kasuwa na NIMPF sun ce akwai kudinsu sama da Naira biliyan 50 a hannun PEF. Shugaban kungiyar ‘yan kasuwan na reshen jihar Kano, Musa Yahaya-Maikifi ya bayyana haka. Musa Yahaya-Maikifi yace muddin aka cigaba a hakan, zai yi wahala man fetur bai yi wahala ba.

Manyan ‘yan kasuwa a Arewacin Najeriya sun kai kuka zuwa ga gwamnatin tarayya a kan bashin Naira biliyan 50 da suke bin tsohuwar hukumar PEF.

Punch ta rahoto cewa:

‘yan kasuwan da suke karkashin kungiyar NIPMF sun koka da cewa bashin zai iya jawo wahalar man fetur a Arewacin Najeriya.

‘Yan kungiyar Northern Independent Petroleum Marketers Forum masu harkar man fetur sun ce jarin da yawa daga cikinsu ya yi kasa saboda rashin kudi. A dalilin wannan bashi na Naira biliyan 50 da ‘yan kasuwan su ke bin hukumar PEF da yanzu an rushe ta, sun ce saye da dakon man fetur ya fara gagaransu. NNN ta rahoto shugaban NIPMF na reshen jihar Kano, Musa Yahaya-Maikifi ya na fadawa ‘yan jarida cewa sun yi watanni tara suna neman kudin na su.

Jawabin Yahaya-Maikifi

“Idan aka cigaba da tafiya a haka, mafi yawan mu za su rufe gidajen mansu. Zai jawo wahalar man fetur a yankin nan saboda ‘yan kasuwa ba su da jari.” “Gwamnatin tarayya ta ki biyanmu kudinmu na sama da Naira biliyan 50. Mun zauna da hukuma, mun nemi su biya mu, amma ba su cika alkawarin ba.” “Shiyasa mu ka zo domin mu nemi alfarma su biya mu hakkinmu domin mu cigaba da gudanar da kasuwancinmu cikin ruwan sanyi.” – Yahaya-Maikifi.

A rahoton da Daily Nigerian ta fitar a ranar Lahadi, Yahaya-Maikifi ya bayyana cewa sun kafa kungiyar NIPMF domin a samu hadin-kan ‘yan kasuwa.

Shugaban na ‘yan NIPMF yake cewa rikicin cikin gidan da barke a kungiyar IPMAN, yana cikin abubuwan da suka sake jagwalgwala halin da ake ciki.

Leave a Reply