Wata mata ta kashe wani da maita

“Sun yi ihu a kaina suna cewa kin kashe shi.”
A lokacin da mahaifin Monica Paulus, ya yanke jiki ya fadi saboda bugun zuciya, dan uwanta ya zargeta da kashe shi ta hanyar maita. An yi ta yi mata barazanar za a kasheta.
Monica ta ce: “Abin ya ba ni tsoro, dukkan kawayena da ‘yan uwana sun guje ni in da suka mai da ni mai muguwar manufa, a lokacin da aka zarge ni na ji matukar kunya ga kuma kyama”.
An tursasa mata barin gidansu inda ta nemi mafaka a wata gunduma da ke Papua New Guinea, wata kasa da ke kudu maso yammacin facific.

Ba abu ne sabo ba a zargi mutum da maita a Papua New Guinea. To sai dai kuma ba za a iya fitar da bayanai a kan adadin irin wanann zargi da ya faru a yankin ba, kodayake gwamnati ta ce an samu irin wannan zargi na maita da suka kai dubu 6 a cikin shekaru fiye da 20 da suka wuce.
Kodayake kididdiga ta nuna cewa adadin zai iya fin haka kuma yawanci mata da yara mataake zargi a duk shekara.
A kan ci zarafinsu, daga nan sai zargi ya biyo baya idan wani ya mutu katsa ham ba tare da wani ciwo ba.
Wata jami’a a hukumar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch Stephanie McLennan, wadda ke aiki a kan irin wadannan zarge zarge ta ce suna kallon tashin hankalin da ya misaltuwa a kan batun zargin mai ta da yadda ake yi wa wadanda ake zargi.
Ana samun ‘yan daba a gari da ke yawan kai wa wadanda aka zarga hari, wani lokaci har kama su suke su ajiye su a wajensu.
Labarin Mary Kopari ya yi fice a duniya a shekarar 2021 bayan kisan gillar da aka yi mata saboda mutuwar wani yaro dan shekara biyu.

Ta kasance tana sayar da dankali a kasuwa a lokacin da ‘yan daban suka kama ta tare da cinna mata wuta har ta kone kurmus.Ba a kama kowa ba a lokacin da abin ya faru.
An yi ta kai wa mata hari amma sun samu sun tsira inda suka gudu zuwa daji in ji Ms McLennan.
Lokacin da Monica ta fuskanci na ta zargin a kan maita, ita ma ta samu ta tsira.
Ta ce,”Da suka zarge ni da kisa ta hanyar maita an kore ni, ba su nemi wata shaida ba.
An hanani na halarci jana’izar mahaifina, na riga na sani bani da wata kafa a wajen iyayena da ma al’ummar garinmu inji ta.
Monica ta yi amanna cewa dan uwanta ya zargeta da kashe mahaifinsu ne saboda ya samu gado shi kadai.

Kungiyar kare hakkin dan adama ta Human Rights Watch ta ce, a shekaru biyu da suka wuce, karuwar kamuwa da cutar korona da aka samu an rinka alakantata da maita.
Inda aka rinka zargin duk mutumin da ya mutu saboda cutar korona sai ace maita ce ta kashe shi in ji McLennan.

A farkon shekarar 2021, ‘yan sanda sun ceci wata mata da ‘yarta bayan an kama su tare da azabtar da su, bayan zarginsu da maita sakamakon mutuwar mijinta saboda cutar korona.
Rahotanni sun ce matar mai sheikara 45 da ‘yarta 19 dukkansu an ji musu rauni har da konuwa a jikinsu.
Gwamnatin kasar a yanzu ta kafa wani kwamiti don dakile irin wannan rikici mai nasaba da maita.

Bayan abin da ya faru da ita, Monica ta sanya rayuwarta cikin hadari wajen kare sauran mutanen da ake zargi da maita.
Ta ce,”Ina ta kokari a kan wannan batu na maita, amma kuma bana ganin wani canji musamman da ake cikin yanayi na cutar korona”.
Monica ta ce a lokacin da take gudun hijra a wani bangare na Papua New Guinea, ta ce a idonta aka jefe wata mata a bayyanar jama’a, wani mutum ne ya yi kokarin yi mata fyade sai ta cire masa harshe daga nan sai a zarge ta da maita.
Ta ce,” A gaban jami’an gwamnati aka kasheta amma ba bu abin da suka yi”.
Monica, ta samar da wata kungiya ta kare hakin mata inda aka kiyasta cewa ta samu ceton mata fiye da 500 a cikin shekara 15.

Monica, ta ce sauyawa irin wadannan mutane wajen zama da kare rayuwarsu abu ne mai muhimmanci, amma kuma akwia bukatar a kwato musu hakkinsu.Idan mutane na ganin ana kwato musu ‘yanci to ba mamaki zarge zargen maita ya ragu”.
Tun da ta fara wannan aiki aka kona gidan Monica, a yanzu ta bar kasar inda ta ke gudun hijra a kusa da Australia.
Ta ce akwai ciwo na yi nisa da ‘ya’yana uku, amma kuma idan har suna cikin lafiya d akwanciyar hankali zan fi kwanciyar hankali, amma kuma akwai ciwo.

 

Leave a Reply