Wata mata ta rasa aikinta saboda tsananin yin ‘Bleaching’

Wata mata ta rasa aikinta saboda kodar da fatar jikinta da kuma zama mai launin fata iri biyu, lamarin da uwar dakinta ta ce bata lamunta ba. Uwar dakin tace koran ya zama dole saboda matar ta yi bilicin har fatarta ta yi fari yayin da yatsunta suka yi baki kirin. A ra’ayin uwar dakin nata, wai bai kamata kwastomomi su ga jikinta da hannayenta na da bambanci ba, hakan zai iya korar su.

Wata ‘yar Najeriya mai suna Ikot Sharon ta ba da labarin yadda wani gidan cin abinci ya bai wa wata ma’aikaciya takardar kora saboda bilicin da rashin daidaito a launin fatarta. Da take ba da labarin dalilin da yasa aka kori matar a shafin Twitter, @IkotSharon ta ce fatar ma’aikaciyar ya yi muni wanda ya haifar da duhun kullin hannayenta wanda ya bambanta da farar fatarta.

Wani bangare na rubutun Twitter din yana cewa:

“Haka wata mata aka koreta yau saboda tayi bilicin sosai, kullin hannayenta sunyi duhu yayin da jikinta yayi fari.”

Ba za ta iya yi wa baki hidima da yadda hannayenta suke ba,dole ta tafi

Bisa wannan rashin daidaiton launin fata, an nuna wa ma’aikaciyar kofar fita domin a cewar uwar dakinta, ba zai yiwu ta iya hidimtawa baki da kodadden jiki tare da kullin hannu mai rodi-ridi.

“Tabbas ba za ta iya yiwa baki hidima da wadancan hannayen ba don haka dole ne mu kore ta.”

Ba na adawa da yin bilicin

Lokacin da wasu daga cikin mabiyanta suka nuna rashin amincewarsu kan matakin da aka dauka na ladabtarwa, ta kare matakin da ta dauka tana mai cewa an baiwa ma’aikaciyar damar sanya safar hannu ko kuma a kore ta amma taki.

“Bana adawa da kodar da fatar jikinki amma dai kiyi shi dai dai, ba ma nuna bambanci ga ma’aikata da kowane irin sharudda, mun yanke shawarin korar ta ne saboda korafe-korafen da ake samu na rashin tsabta, ta ki yarda.”

“Safar hannu ma zabi ne a gare ta. Muna gudanar da binciken lafiya akan duk ma’aikatanmu kuma muna nemo mafi kyawun hanyoyin sarrafa su tare da mu.

“Mun yi yadda zamu fitar da ita daga wurin amma ta ki saboda an dauke ta a matsayin “waitress”. Ba mu kyale ta ta tafi ba tare da kokarin yin tunani akanta ba kuma mun yi la’akari da sha’awar kwastomominmu.” Kodar da fata al’ada ce da ta mamaye tsakanin mata masu duhu. Rahoton Fabrairu 2021 na The Conversation ya nuna cewa mata masu duhun launin fata suna kashe kusan dala biliyan 8.6 kowace shekara don yin bilicin fata.

Leave a Reply

Your email address will not be published.