An yi wa Yusuf Buhari, da namiji daya tilo na Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, nadin sarauta matsayin Talban Daura kuma Dagacin Kwasarawa.
Wannan bikin nadin sarautan ya gudana ne a mahaifar garin Daura, jihar Katsina Yau Asabar, 18 ga Disamba 2021. Daga cikin wadanda suka halarta akwai Mataimakij Shugaban kasa, Yemi Osinbajo; Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan; da Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
Sauran sunr Ministan Sufurin jirgin sama, Hadi Sirika; Ministan Neja Delta, Godswill Akpabio; Ministan Kimiya da Fasaha, Ogbonayya Onu; da Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero.
Hakazalika dimbin Sanatoci da mambobin majalisa.