FALALAR ZUWA MASALLACIN JUMA‘A DA WURI 

Assalamu alaikum.

Da yawa mukan shagalta da wasu al‘amura na rayuwar duniya har mu kwashe lokaci mai tsawo ba tare da mun damu ba, amma cikakkun awowi biyu (2hrs) ba zamu iyayi a wurin bautar Allah cikin nishad‘i ba.

A ranar Juma‘a ana son zuwa Masallaci da wuri domin samun babbar rabo.
Ankar‘bo Hadithi daga: Abu Hurairah (RA) yace: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: Duk wanda yayi wanka, sannan ya tafi Masallacin Juma‘a (da wuri), yayi Sallah (ta nafila) gwargwadon abinda ya samu, sannan ya saurara, har Liman ya fito domin yin Khudubah, ya saurari Khudubah aka yi Sallah tare da shi: to, an gafarta masa abinda ke tsakanin Juma‘ar da kuma wata Juma‘a mai zuwa, tare kuma da bashi falala ta kwanaki uku.
[MUSLIM]
Zuwa Masallacin Juma’a da Wuri Yanada Tarin Lada Mai Yawa.
Manzon Allah (S.A.W) yana Cewa: Wanda Yayi Wanka a Ranar Juma’a, Sannan ya Tafi Zuwa Masallaci a Farkon Lokaci, Yanada Lada kamar Yayi Sadaka da Rakumi. Idan Yaje a Sa’a ta Biyu, kamar yàyi Sadaka ne da Saniya. Idan Yaje a Sa’a ta Uku kamar Yayi Sadaka ne da Rago. Idan Yaje a Sa’a ta Hudu kamar Yayi Sadaka ne da Kaza. Idan Yaje a Sa’a ta Biyar kamar yayi Sadakane da Dabino. Idan Liman Yazo Ya Hau kan Mimbari, Sai Mala’ikun su Rufe Takardunsu su tsaya Suna Sauraran Khuduba.
Bukhari (841) da Muslim (850)
Wanda ya tafi a kasa zuwa Sallar Juma’a Yana Samun Ladar Azumin Shekara Guda da tsayuwar dare na Shekara Guda ga Kowane taku.
Daga Ausi bn Ausi (r a) Daga Manzon Allah (s.a.w) Yace: Dukkan Wanda Yayi Wanka a Ranar Juma’a (Wankan Juma’a), Yayi Sammako Yaje da Wuri, ya Zauna ya Saurari khuduba yayi shiru beyi Magana ba, Ya kasance yana da Lada ga Kowane Taku da Yayi Zuwa Masallaci, Yanada Ladar Azumin Shekara Guda da tsayuwar dare na Shekara Guda.
ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ‏( 410 ) .
ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴﻢ ﻓﻲ ﺯﺍﺩ ﺍﻟﻤﻌﺎﺩ ‏( 1/385 ) :
Yana Cewa: *Imam Ahmad* Yana Cewa: Wannan Wankan Yana Bayyana Mana Mustahabbine ga Mutumin Daya tara da Iyalinsa a Ranar Juma’a.
ﺍﻟﺤﺎﻓﻆ ﺍﺑﻦ ﺣﺠﺮ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ
Bayan Ya Jero Hadisan Falalar Sallar Juma’a Sai Yace: Abinda Muka kawo na Falalar Juma’a Na Kankare Zunuban Juma’a Zuwa Wata Juma’ar da sauran falala. Hakan baya tabbata ga bawa sai ya Cika wadansu Sharudda Wanda suka zo Acikin Hadisan kamar:
1. Yin Wanka da tsafta dan zuwa sallar juma’a.
2. Sanya tufafi mai kyau da sanya turare da shafa mai.
3.Tafiya cikin Natsuwa zuwa Masallaci.
4. Barin Qetara Tsakanin Mutum Biyu da Rashin Cutar da Mutane a Masallacin.
4. Dayin Shiru Lokacin khuduba.
Saboda haka ‘Yan‘uwa mu dinga zuwa Masallaci da wuri.
Allah ya bamu ikon gyarawa (Ameen)

Leave a Reply

Your email address will not be published.