Babban Magana: Adebanjo ya bukaci EFCC ta binciki dukiyar Bola Tinubu da Bisi Akande

Shugaban kungiyar yarbawa, Afenifere, Chief Ayo Adebanjo, ya caccaki tsohon shugaban APC, Bisi Akande, kan cewa ya roki jagoran APC, Bola Tinubu, ya gina masa gida a Lekki.

Punch ta rahoto cewa shugaban Afenifere, ɗan kimanin shekara 93 ya bayyana yadda ya tara kudinsa har gina gidan wanda yake zaune a ciki yanzu haka.

Adebanjo ya bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gudanar da bincike kan hanyoyin samun kudin Tinubu da Akande.

Mista Adebanjo ya yi wannan furuci ne a wurin taron manema labarai a Legas, ranar Alhamis, a wani martani ga zargin da Bisi Akande ya masa a cikin litafinsa mai fegi 559.

Cikakken bayani na nan tafe…

Leave a Reply