Wani Sarki yayi wuff da ‘yar shekara 20

Daily Nigerian ya ruwaito cewa Mai Martaba Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk, ya yi sabuwar Amarya, Aisha Iro Maikano, a ranar Asabar.

An tattaro cewa an yi daurin auren bayan dan gajeren lokaci da Sarkin ya hadu da yarinyar wacce diya ce ga Fagacin Katsina, Iro Maikano.

Hakazalika rahoton ya nuna cewa an daura auren bisa kudin sadaki N1million.

Wani gajeren bidiyo ya nuna yadda Amaryar ke tika rawa.

Hakazalika rahoton yace Magajin Garin Daura ne ya wakilci Sarkin wajen bikin daurin auren.

Leave a Reply