Sallar al-Kunutu da yadda ake yin ta

A baya-bayan nan an yi ta samun kiraye-kirayen gabatar da addu’ar Al-ƙunutu a Najeriya, domin roƙon Allah Ya kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ta addabi musamman yankin arewacin ƙasar.

Daga kan Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya Muhammad Sa’ad Abubakar III zuwa kan ƙungiyoyin addinai irin Izala da ma ɗaiɗaikun mutane da suka dinga wannan kira a shafukan sada zumunta.

“Wannan kiran ya zama dole idan aka duba yadda ake ci gaba da kashe rayuka da wulaƙanta su gabagaɗi kamar yadda muka gani a Sokoto da Gidan Bawa da Beni-sheikh da Kaga (Jihar Borno),” a cewar sanarwar da sakataren Jama’atu Nasril Islam Dr. Khalid Abubakar Aliyu ya sanya wa hannu.

Tun daga farkon makon da ya gabata ‘yan fashin daji sun ƙona mutum 23 da ransu a cikin motar fasinja a Jihar Sokoto.

Sannan ‘yan bindiga sun kashe mutum aƙalla 15 a masallaci a Jihar Neja; an kashe kwamishina a Jihar Katsina a cikin gidansa.

A wannan maƙalar, BBC ta yi duba kan mece ce Al-Kunutu, yaushe ake yin ta, kuma yaya ake yin ta. Mun tuntuɓi malamai don amsa waɗannan tambayoyi.

Shin me ake nufi da Al-Kunutu?

Sheikh Tijjani Bala Kalarawi, malamin addinin Musulunci ne a Najeriya, ya bayyana cewa al-Ƙunutu addua’a ce da ake yi a lokacin da wani bala’i ko musiba suka fada wa al’umma.

A ƙasƙantar da kai da miƙa lamari ga Allah SWA.

“Ana yin sallah raka’a biyu ko gwargwadon hali, ana kuma karanta duk surar da ta sawwaka baya ga Fatiha, sannan a raka’a ta karshe ana so Musulmi ya miƙa lamarinsa wajen Allah da rokon neman sauki daga gare shi kan wata musiba ko bala’i da ya afka wa musulmi.

Babu wata sura ta musamman da aka ware ko addu’a ta musamman da a sallar al-Ƙunut ne kadai ake yin su.

Musulmi yana damar karanta surar da ta sawwaƙa ko wadda ya sani, ya kuma yi addu’a gwargwadon iliminsa duk dai abin da ake nema shi ne, samun sauki da agajin Allah SWA a kan wani hali da jama’a suka samu kansu a ciki,” in ji Malamin.

Wadanda suka kamata su yi al-kunut

Ibada umarni ne daga Allah Madaukakin Sarki zuwa ga bayinSa. Don haka kowanne Musulmi yana da iko da damar da zai yi wannan sallah ta al-Ƙunutu.

Ana kuma yin ta ne sakamakon fadawa cikin wata musiba. Ba a yin al-Ƙunutu idan wata annoba ta faru, misali annobar korona, ko fari, ko talauci da makamantansu.

Nau’o’in Al-Kunut

Akwai nau’o’i biyu na Sallar al-Kunut.

1. Akwai nau’in al-Kunutu wadda ake yin ta a raka’ar karshe ta Sallar Asuba, kafin ruku’u ko bayan ruku’u. Wadda ita ce manzon Allah SAW ya yi ta har karshen rayuwarsa.

Kuma ita ce wadda Sahabbai suka yi koyi da shi, bayan wafatinsa suka ci gaba da yin ta a ko da yaushe.

Ita ce wadda masu bin mazahabar Malikiyya suka ci gaba da yinta, a duk inda garuruwan da ake bin mazahabar ta malikiyya a zamanin sahabbai da tabi’un.

2. Akwai kuma al-Kunutul Nazila, ita ce wadda ake yin ta idan wata musiba ko bala’i ya taso wa al’umma. Wadda ita ce Manzon Allah SAW ya yi ta tsawon lokaci, ko ana zaman lafiya ko ba a zaman lafiya.

Su wane ne ke yin al-Kunut?

Sheikh Hussaini Zakariyya, malamin addinin Musulunci ne a babban birnin Najeriya, Abuja, ya kuma shaida wa BBC cewa: “An fara yin Sallar al-Ƙunut ne tun zamanin Annabi Muhammad SAW, kuma da kansa ya fara yin ta SAW.

A shekara ta hudu bayan hijira an zalunci Musulmai an kashe su ba kadan ba, domin haka sai Annabi Muhammad SAW ya fara wannan addua ta al-Ƙunut.

Manzon Allah ya shafe wata guda yana yin ta daga bisani ya daina, sakamakon wahayin da Allah SWA ya saukar inda ya umarci ya daina. Wannan bayani na cikin Suratu Ali Imran, aya ta 128, in ji malam.

Sheikh Hussaini Zakariya ya ƙara da cewa, ƙaulin malamai ya zo da cewa tun bayan al-Ƙunutun da Manzon Allah SAW ya yi a shekara ta hudu da yin hijira, ba a kara yin ta ba har ya koma ga Allah.

Haka kuma a zamanin Sahabbai, irinsu Sayyadina Abubakar, da Umar, da Usman, da Ali, duk kuwa da cewa an shiga bala’i da musibu daban-daban amma ba a yi al-Ƙunutu ba.

Misali an shiga musiba a zamanin Sayyadina Usman da aka shafe shekaru shida cikin tashin hankali, da zamanin Sayyadina Ali RA da aka yi ta samun kashe-kashen Musulmai da rarrabuwar kawuna a tsakaninsu duka ba a yi wannan al-Ƙunutu ba.

Sannan an yi annoba a lokacin zamanin Sayyadina Umar, wadda ta janyo mutuwar sahabbai da dama, amma babu inda aka ambaci cewa an taru a masallatai an yi ta yin al-Ƙunutu.

Malam Zakariyya ya ce malamai sun kasu kashi biyu a kan wannan batu, akwai wadanda suke ganin bai kamata baki daya a yi al-Ƙunutun ba, wasu kuma na cewa za a iya yi amma wadda ake yin ta cikin sallah ta biyan bukatu.

Ya kuma zo a nafsi cewa hatta malaman Malikiyya da Hambaliyya ba su karfafa yin ta ba, wanda ke ganin bidi’a ce tun da Manzon Allah SAW ya bar ta bai kamata a ci gaba da yi ba.

Akwai kuma malaman da suke ganin za a iya yi, amma dai duka sun hadu akan kaulin cewa al-ƙunutul Nazila ba farilla ko sunna ba ce, ta fada mustahabbi.

Yaya ake yin al-kunut? 

Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya shaida wa BBC cewa babu wata hanya guda daya da aka ware kan yadda za a gudanar da Sallar al-Ƙunutu, sannan babu wata sura ta musamman da aka warewa wanda zai yi Sallar al-Ƙunutu, hasalima ba a bayyane ake yin ta ba.

“Duk abin da ba Al-kur’ani ba makaruhi ne a bayyana shi cikin sallah ta farilla, ita kuma al-Ƙunutu, ana yin ta ne a raka’ar karshe ta sallar farilla, don haka ba a yin ta a bayyane.

“Abu muhimmi a wannan halin da ake ciki shi ne, kowa ya koma ga Allah a duk sallolin farilla ko nafila, ba lallai sai an taru a wuri guda an yi hakan ba,” in ji malam.

Shi ma Sheikh Hussaini Zakariyya ya ce akwai wadanda suke ganin baki daya ma al-Ƙunutu, da ake yi bayan sallolin farilla, bai halatta a yi ta bayan Sallar Asubahi ba, akwai masu ganin za a iya yin ta har tsawon rayuwa.

Yayin da malaman da ke bin mazahabar Malikiyya da Shafi’iyya da suka yi bayanin ba a yin al-Ƙunutu bayan shafa’i da wuturi, sai a cikin watan Ramadan a sha biyar din karshe.

Batun Sallar al-Ƙunutu batu ne mai cike da sarƙaƙiya, idan aka yi rashin sa’a mutum bai dauki darasin a wajen malamai ba sai a samu matsalar rashin fahimta.

A karshe, Hussain Zakariya ya ce, mabiya azhabar Imam Ahmad Bin Hambal, suna ganin ana yin wannan sallah ta al-Ƙunutu.

Sannan tarihi ya nuna cewa a zamanin sahabbai da tabi’ai da ke zaune a Madina ba sa yin wannan al-Ƙunutu a cikin Madina, amma wasu da suka je kasashe kamar Misra sun ci gaba da yin hakan.

Leave a Reply