Gwamnati ta bayyana sunayen kungiyoyin da ke daukar nauyin ta’addanci

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (rtd), ya bayyana sunayen kungiyon da ke daukar nauyin ta’addanci a Najeriya sauran kasashen Sahel.

A cewarsa

Jama’at Nasr al-Islam Wal Muslimin (JNIM), Islamic and Muslim Support Group (GSIM) da ISGS sune kunyoyin da ke karfafa ayyukan ta’addanci, The Nation ta ruwaito.

NSA ya bukaci masu wa’azin addinin Islama da Limamai da su dauki matsaya mai kyau don tallafawa ayyukan gwamnati a yaki da ta’addanci. Ya lura cewa kawance tsakanin malamai da jami’an tsaro “ya zama kashin bayan sake gina al’ummominmu da ta’addanci suka mamaye”. NSA ya yi wannan jawabi ne a wajen taron karawa juna sani na kungiyar Malamai da masu wa’azi da limaman kasashen Sahel karo na 14 a Abuja.

Yace:

“Ta’addanci da karuwar ayyukan ta’addanci daga kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin Islama a yankin Sahel tun daga shekarar 2016, kungiyar Islamic State in Greater Sahara (ISGS) ce ke jagorantarsu, wadda galibi ke aiki a Mali har zuwa Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso. “Ayyukan kungiyoyi irin su Jama’at Nasr al-Islam Wal Muslimin (JNIM), Islamic and Muslim Support Group (GSIM) da ISGS, ke ci gaba da yin barazana ga zaman lafiyar yankin. “A Najeriya, kungiyar Boko-Haram da kungiyar Islamic State of West African Province (ISWAP) ne suka mamaye ayyukan ta’addanci, musamman a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Leave a Reply