Mutane da dama anyi musu kutse (hacking) a account dinsu na Facebook, Instagram da sauransu. Kutse wato hacking da turanci shine shiga account din wani ba tare da izinin shi ba. Kutse (Hacking) ya yawaita wa accounts din yan-uwa musamman a Facebook.
Duk wani kutse (hacking) da za’ayi a Duniya, ya ta’allaqa ne ga abubuwa 2:
IP address (Internet Protocol) da kuma PASSWORD.
Don yin kutse (hacking) ma Facebook din wani, kanada buqatar USERNAME da PASSWORD dinsa, amma samun Username baida wahala, sabida mafi yawa zaka sameshi a Timeline din mutum, matsalar itace Password!
YADDA ZAKA KIYAYE ACCOUNT DINKA
1. Ka hada Password mai wahala: ya zamana Password dinka yakai haruffa 8 ko sama da haka, ya zamana ka chakuda haruffa da lambobi, kada ka saka sunanka, sunan dan-uwanka ko wani makusancinka, kuma ka chakuda Upper-case da Lower-case (Manyan baqi da qanana) misali: P3hkT5so. Ka sani, iya tsawon password dinka, iya wahalar da zai ba Hackers wajen maka kutse.
2: Akwai wani tsari na REMEMBER-PASSWORD dake kan Opera mini browsers, a bisa wannan tsari, duk sanda kai logging a wani shafin internet ka sanya Username dinka da password, zasu ce maka: Remember Username and Password? Idan ka danna OK, shikenan zasuyi saving dinsa, duk sanda kahau facebook, zai dinga budewa Automatically ba tare da buqatar ka saka Pasword ba!
Haqiqa wannan tsari na da Hatsari, domin duk sanda wani ya dauki wayarka, da zarar ya bude opera, zai iya hawa account dinka, hakanan in ka siyar da wayarka, ta fadi/aka dauketa. Don haka kada ka dinga zaban wannan tsari, idan kuma ka zabeshi, to ka gogeshi ta hanyar: OPERA=>SETTINGS=>PRIVACY=>REMEMBER PASSWORD=OFF/NO/UNSELECT! Sannan sai ka dawo qasa zakaga CLEAR PASSWORD=>YES!
3: Akwai Hackers dake turo da message na shirme (Spam/Trujars/Trash), duk sanda kaga message daga mutuminda baka sani ba, ko kaga Alamun ba dan Qasarka bane, to kada ka bude, in ka bude kuma, kada ka masa Reply, da zarar ka masa Reply, zai iya samun damar kutse wa account dinka.
Yanzu abin ya shigo Nigeria sosai, ku kula da irin mutanen dake turo sako (message): Hello/Hi, zaku gansu da turanci suke, sannan profile dinsu is incomplete (bai cika ba. Za ku ga wasu lokutan ba hoto, ko kuma akwai hoto na bature ko kuma Wanda ba dan ‘kasa ba).
4: Akwai Applications da dama da zaka shiga, ace maka ENTER-YOUR FACEBOOK USER NAME AND PASSWORD: Kada ka sake ka rubuta! Sannan akwai sites da za kaga musamman in kahau Facebook, za su ce meka: WE WILL USE YOUR FACEBOOK USERNAME AND PASSWORD (Za muyi amfani da Username da Password dinka na facebook). To kada ka sake ka amince, ka fice kawai, da dama, sune suke sanya hotunan Batsa, rubuce-rubucen banza a profile din mutane, domin duk sanda ka amince musu, shikenan sunada damar Posting a profile dinka, Tagging Friends dinka da tura musu sa’ko (Message).
5: Ka dinga sake Password dinka duk wata, kuma ka dinga hada password da zasuyi wahalar chinka.
6: Duk sanda zaka sauka a Facebook, ka dinga LOG-OUT kafin ka rufe browser dinka.
7: Kada ka dinga Log-in (hawa Facebook) ta computer din kampani, Cafee, wayar wani da sauran su. Idan kuma ka hau, ka tabbata kayi log-out kan ka sauka, in so samu ne, da zarar ka dawo gida, to ka sake password dinka.
8: kada ka dinga Accepting Friends da baka sani ba, Musamman kaga India, China ko wata qasa. ko kuma kaga profile dinsu bai cika ba, kaman kaga suna ne kawai, amma ba sauran bayanan mutum (details). Ka kiyayi irin wadannan Profiles din, dayawansu masu kutse (Hackers) ne.
9. Ka saka email dinka a account dinka na Facebook. Wannan shine yafi komai mahimmanci. Za’a iya cire maka numban wayanka, amma yana da wahala a cire maka email daga account dinka na facebook. Sannan ta email din za ka iya dawo da account dinka in anyi hacking dinsa.
- A duk sanda kayi sakaci da Account dinka, har wani yayi yunqurin hada Password dinka, da zarar yayita trying, Facebook zasuyi blocking Account din for security, sannan zasu sanar dakai duk sanda kazo Hawa FB, zasu buqaci ka sake Password!
Anan zanso inba Yan-uwa shawarar: Idan ka bude FB dinka ne da Email, to ka tabbata email din na aiki, kuma ka kula dashi sosai, domin duk wani aiki da ya shafi Account din, zai ci gaba ta email..
Idan kuma da Lambar waya ne, to ka tabbata lambar da kayi amfani da ita tana aiki, in ka sake lamba, to kayi maza ka sake lambarka a facebook: SETTINGS=>CONTACT INFORMATION=> a qasa zakaga wajen Number, bayan ka saka lambar, akwai za’bi (Option) da zasu baka, na wadanda kake so suga lambar, don kariya, ka zabi: ONLY ME!
*Sannan akwai wani tsari na TRUSTED CONTACTS: wannan tsari zai baka damar zaban abokanka na facebook da ka aminta dasu, in so samu ne, su zama suna kusa dakai, domin duk sanda account dinka ya samu matsala, kuma ya zamana baka da email ko na ka ya daina aiki, ko lambar da ka bude FB ya fad’i, to ta hanyarsune zaka iya dawo da account dinka, kuma zaka iya saka daga mutum 1 zuwa 10. Don saka mutum: SETTINGS=>SECURITY=>TRUSTED-CONTACTS=>ENTER YOUR PASSWORD (anan zaka rubuta password dinka, domin FB su tabbatar da kaine ba wanine ya hau account din ba)=>ADD CONTACT (sai ka zabi wanda kake so)=>SAVE.