Wani matashi ya biya dala daya (N409.89) a matsayin kudin sadaki/

Bernard Musyoki ya hadu da masoyiyarsa Jan Spicer a Facebook a shekarar 2017 kuma suka fara soyayya. A ranar 29 ga Disamba, 2020, Matar ta yanke shawarar zuwa Afrika domin haduwa da masoyinta Bernard Musyoki ya ce lokacin da ya fadawa mahaifiyarsa zai aureta, sai da tambayeshi shin za ta haihu.

Bernard Musyoki wani matashin da ya auri Ba-Amurkiya yar shekara 70 yace mutane na sukansa kuma suna zarginsa da cewa kawai yana son zuwa Amurka ne.

A hirar da yayi da jaridar TUKO.co.ke, ya bayyana cewa shi kawai yana sonta ne kuma sadakin akwai rahusa.

Yadda suka hadu

Musyoki wanda dan jihar Kitui ne a Kenya ya bayyanawa jaridar TUKO.co.ke cewa ya hadu da Deborah ne a manhajar Facebook a shekarar 2017.

A cewarsa:

“Ni na bukaci mu fara kawance, bayan mako guda, nace mata ta aure ni kuma ta amince.”

Kudin sadaki

Yace basu daina tattaunawa da juna ba har karshen Disamban 2020, matar ta yanke shawaran zuwa Kenya domin haduwa da shi.

Yace:

“Muna bacci a dakuna daban-daban kuma mun yi alkawarin ba zamu yi jima’i ba har sai an daura mana aure.”

“Maganar sadaki sun ce kawai in kai N409.89 coci matsayin sadaka kuma tace min sadakin kenan.”

Yan Najeriya sun yi tsokaci:

Fatima Ta Annabi tace:

“Talauci masifane wannan ai tsiyace sa’ar kakarshi,Allah yakyauta.”

Æthëærmu Prësdœr:

“Hhhhhh to wlh Koni yadda nake Shan luguden wahala a Nigeria dana samu wacce zatayi wup Dani wallah Ina fecewa.”

Zainab Yusuf tace:

“Hmmmm… Ba dole yaso taba, ita ba dole tasoshi ba, Abar kaza cikin gashin ta kawai.”

Hauwau Muhammad tace:

Kamar na dankara ashar wallah Wai soyayya, nabi soyayya da dan banzan gudu na naushi keyar ta da katako tirrrrr.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.