Wani mai gadi ya zama shugaban Kasa

An soma wallafa wannan labari ne ranar 2 ga watan Disambar shekarar 2016.

Hukumar zabe mai zaman kanta a Gambia ta sanar da Shugaba Adama Barrow a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da aka gudanar a ranar Asabar.

Alkaluman da hukumar zaben kasar Gambia ta fitar ya nuna cewa, Mista Barrow ya samu kuri’u kusan sau biyu fiye da wanda babban abokin hamayyarsa Ousainou Darboe ya samu (53% zuwa 28%).

Adamu Baro ya lashe kuri’u 457,519 yayin da dan takarar jam’iyyar adawa Ousainou Darbor ya samu kuri’u 238,253.

Shugaban kasar Gambia, Adama Barrow, fitaccen mai saye da sayar da gidaje ne, wanda bai taba rike wani mukami na siyasa ba kafin kayen da ya yi wa Shugaba Yahya Jammeh a zaben watan Disamba.

An haife shi ne a shekarar 1965 a wani kauye da ke kusa da garin kasuwancin nan na Basse a gabashin kasar.

Kafin a tsayar da Mr Barrow, mai shekara 51, a matsayin dan takarar shugaban kasar, ya kwashe sama da shekara goma yana hada-hadar gidaje.

Ya zauna a London a shekarun 2000, lokacin da yake karatu kan harkokin gidaje, kuma a lokacin ne ya yi aiki a matsayin mai gadin babban kantin nan na sayar da kaya, Argos a arewacin London.

A wancan lokacin ne ya soma goyon bayan kungiyar kwallon kafar Arsenal.

Ya koma kasar Gambia a shekarar 2006 inda ya soma kasuwanci a fanni gine-ginen gidaje.

A lokacin da yake yakin neman zabe, Mr Barrow ya sha sukar Shugaba Jammeh kan rashin sanya wa’adi biyu kawai ga duk wanda zai shugabanci kasar sannan ya soki daurin da aka yi wa ‘yan jam’iyyun hamayya.

Mista Barrow yana fafutikar ganin bangaren shari’a ya samu ‘yanci sannan ‘yan jarida da kuma kungiyoyin farar-hula sun samu damar fadin albarkacin bakinsu ba tare da wata shakka ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.