Ɗan iska ya zama matukin jirgin sama

Wani ma’abocin amfani da manhajar Twitter, @_deoluwaa ya bayyana yadda wani da su ka yi aji daya dashi a sakandare yana shaye-shaye ya zama matukin jirgin sama. A cewar @_deoluwaa, a lokacin babu wanda yake ganin matashin da mutunci amma yanzu ya daukaka, yayin da ya bar su shiryayyun ba su da ko sisi. Bayan mutane da dama sun ga wannan wallafar ta shi, sun yi ta cece-kuce inda kowa ya dinga tofa albarkacin bakinsa, hakan ya sa muka wallafa wasu daga cikin tsokacin.

Wani matashi wanda ya kira kansa da “talaucinka ya yi yawa da a kai kararka” a kafar sada zumunta, mai amfani da suna @_deoluwaa ya yi wata wallafa a kafar sada zumunta wacce dubannin jama’a su ka dinga tsokaci karkashinta.

A cewarsa, ya na da wani da su ka yi aji daya da shi a sakandare, kuma a lokacin kowa yana yi masa kallon tantirin dan iska.

Kamar yadda mutumin ya wallafa: “Dan ajinmu a sakandare wanda ake jan kunnen yara daga bin shi. Yana shaye-shaye tun lokacin da muke aji biyu zuwa na uku a sakandare.” Abin mamaki, matashin wanda ya ce a yanzu shi ba mai hannu da shuni bane, ya bayyana cewa abokinsa, wanda a baya shine ‘dan iskan’ aji yanzu ya zama matukin jirgin sama kuma attajiri. “Abin da zai baka mamaki shine yadda yanzu ya daukaka ya zama matukin jirgin sama a Amurka. Ni kuma wanda na fi kowa hazaka da halaye na gari banda komai.”

Tsokacin jama’a

Mutane da dama sun dinga yin tsokaci iri-iri karkashin wallafar.

DanielRegha ya ce:

“Farkon abinda ya dace iyaye su yi shi ne su koya wa yaransu dabi’u na kwarai kuma abinda iyayenka su ka yi kenan, sun ja kunnenka akan masu shaye-shaye. Batun kuma dauka a rayuwa, ba wani abu bane. Ka daina hada rayuwarka da ta wani saboda baka san abinda su ka yi ba da suka samu wannan daukakar.”

Deoluwa ya ce:

“Ban fahimci abinda mutane su ke daukar arziki ba. Wannan fa abu ne na duniya. Idan ka so ka ba danka kyautar sigari ranar da ya cika shekaru biyar, kai ka sani.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.