Yadda ake cike fom din shiga aikin dan sanda a yanar gizo 2021.

Hukumar yan sandan kasar nan, ta sanar da bude shafin yanar gizo domin ɗaukar sabbin ma’aikata 2021. Mun tattaro muku duk takardun da ake bukata da kuma bayani kan yadda zaka cike fom ɗin ba tare da kuskure ba. Hukumar ta kuma baiwa yan Najeriya masu sha’awar shiga aikin makonni shida su kammala cike bayanan su, su tura mata kai tsaye.

A yau Litinin 29 ga watan Nuwamba aka fara ɗaukar sabbin jami’an yan sanda na shekarar 2021.

Wannan na kunshe a wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na Facebook ɗauke da sa hannun kakakinta, Frank Mba. Sanarwan wacce akaiwa take da ‘Ɗaukar sabbin jami’an yan sanda 2021,’ Hukumar tace waɗan da suka samu nasara zasu zama sabbin yan sanda.

Neman shiga aikin ɗan sanda a shafin da hukumar yan sanda ta buɗe zai shafe makonni 6, fara wa daga yau Litinin 29 ga watan Nuwamba, 2021 zuwa 10 ga watan Janairu, 2022.

Bayan mutane sun kammala cike fom din shiga aikin, hukumar zata gayyaci waɗan da suka samu nasara zuwa wurin tantancewa daga 10 zuwa 24 ga watan Janairu.

Abubuwan da ake bukata

Mun tattaro muku takardun da ake bukatar kowane mai neman aikin dan sanda ya tabbata ya mallaka

1. Lambar katin zama ɗan ƙasa (NIN), adireshin tura sako na Email wanda ke aiki, da lambar wayar salula.

2. Ya zama wajibi kana da mafi karanci credits 5 a zaman jarabawar gama sakandire da bai wuce biyu ba na WASSCE/GCE/NECO/NABTEB. Amma dole ne ka ci Turanci da Lissafi.

3. Kwafin takardan kammala sakandiren ka na asali zaka saka a shafin yanar gizo.

4. Wajibi ne mai neman aiki kada ya gaza shekara 17 kuma kada ya wuce shekara 25.

5. Wajibi ne duk mai neman aikin ya kasance mai cikakkiyar lafiya ta fili da ta boye. Kuma namiji kada ya gaza tsawon mita 1.67m, mata kuma sai kin kai tsawon mita 1.64 zuwa sama.

Dalla-Dalla yadda zaka cike fom ɗin nema aikin Da zaran ka kammala haɗa waɗan can abubuwan da muka zayyana a sama, sai ka ziyarci shafin www.policerecruitment.gov.ng, ka cike fom ka tura.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.