Matar da jininta ya gagari cutar HIV

Wata mata ‘yar Argentina ta zamo ta biyu a duniya da ta yaki cutar HIV mai karya garkuwar jiki, ba tare da shan kowanne magani ba. Likitoci sun yi amanna da cewa garkuwar jikin matar ce ta kakkabe cutar daga cikinta.

Rahoton da mujallar Internal Medicine ta wallafa, bayanin gwaje-gwajen da aka yi wa matar sun gano garkuwar jikinta ce ta fatattaki kwayar cutar.

Kwararru sun ce indai aka ci gaba da samun masu yakar cutar irin hakan, zai kawo sassaukar hanyar yaki da cutar HIV.

Kakkabe cutar HIV

Binciken ya gano ana halittar tsirarun mutanen da garkuwa jikinsu ke yakar cutar HIV.

Wasu kuma su na da garkuwa ta musamman da ake gadonta. Ciki har da wadanda sam cutuka masu yaduwa ba sa kama su, da kuma ba sa son as an da su.

Yawancin mutanen da suka kamu da cutar HIV, rayuwarsu na dogaro ne ga shan magunguna. Idan suka daina shan maganin, garkuwar jikinsu na yin rauni tare da karawa kwayar cutar karsashi daga nan kuma sai wata matsala ta faru.

A shekarun baya, an samu rahotannin samun wani maganin da zai karya laggon cutar HIV, ba tare da shan ainahin wadancan magungunan ba.

Adam Castillejo, daga birnin London, ya daina shan maganin cutar HIV, bayan an yi masa dacen kwayoyin halitta don maganin cutar daji da yake fama da ita.

A lokacin da ake yi masa gashin kashe cutar kansa, aka yi nasarar kashe kwayoyin cutar HIV da yake dauke da ita.

Abin damuwar shi ne ana samun kashi 1 na masu kwayoyin halitta irin wanda ya taimaka masa.

Sai dai babu tabbas din tsawon lokacin da wannan hanya za ta yi wa Mista Castillejo aiki.

Kashe kwayoyin cuta

Sai dai ba a samu alamun kwayar cutar HIV a jikin maras lafiyar Esperanza har tsawon shekara 8.

Ita ma Loreen Willenberg, daga San Francisco, alamu sun nuna garkuwar jikin ta ta yi yaki da cutar HIV, sam ba ta dauke da ita.

Wannan ya sanya an samu kyakkyawanb fatan da ke nuna za a iya amfani da hanyar kashe kwayar cuta domin magance cutuka masu yaduwa.

Jagoran binciken Dakta Xu Yu, daga cibiyar bincike ta babban asibitin Ragonf a Massachusetts, wanda aikin hadin gwiwa ne tsakaninsu da cibiyar binciken kimiyya ta Massachusetts ta ce: “Akwai matakin da za a iya dauka na inganta amfani da hanyar kashe kwayoyin cuta, ta yadda mutanen da ba su da garkuwar jikin da za ta yaki kwayar cutar da suke dauke ta da ita.

“A yanzu mu na duba yiwuwar gabatar da irin wannan hanyar, ta amfani da allurar rigakafi, da nufin gabatarwa da garkuwar jikin marasa lafiyar wani bakon abu, ta yadda za a iya shawo kan kwayar cutar.”

Kwayoyin cutar da za a iya zubarwa

Farfesa John Frater, na jami’ar Oxford, ya shaidawa shirin BBC News, cewa ya yin da ake ganin kwata-kwata babu wata hanya ta magance cutar HIV, amma sai gashi masu binciken sun gano wata hanyar ta daban, ana bukatar ci gaba da bincike domin gani karin hanyoyin warkar da cutar.”

“Babbar tambayar ita ce shin marasa lafiyar da kan ta ta yi magani, ko kuma sun yi amfani da hanyoyin magance cutar, ko an gano su na da cutar akan lokaci akai magani,” in ji shi.

“Garkuwar jikinta ta nuna karara, an taba samun kamuwa da cutar, dan haka babu batun tambayar ko ta taba kamuwa da ita.

“Watakil an taba samun wasu marasa lafiyar da suka yaki cutar ta wata hanyar, amma ba a san da su ba, dan haka ana bukatar fadada bincike.”

Farfesa Sarah Fidler, kwararriya kan cutar HIV a kwalejin Imperial da ke London ta wannan bincike zai taimaka wajen bunkasa hanyoyin yaki da cutuka masu yaduwa, musamman a halin da ake ciki na neman hanyoyin magance cutuka masu yaduwa ba lallai sai an yi amfani da magungunan da akan dora maras lafiya akai ba, ciki har da cutukan da masu dauke da su ke kare rayuwarsu a shan magani kamar dai cutar HIV.

Leave a Reply

Your email address will not be published.